
Alfijr ta rawaito akalla fasinjoji 20 ne suka kone ƙurmus a wani haɗari da ya afku a mahaɗar Maya/Lanlate da ke Ƙaramar Hukumar Ibarapa ta Gabas a jihar Oyo ranar juma a
Alfijr Labarai
Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya tattaro cewa lamarin ya haɗa da wata motar haya ƙirar bas da wata mota ƙirar Sienna.
Motocin guda biyu na tafiya ne ta gaba da gaba, inda suka yi taho mu gama da juna, inda motocin suka kama wuta nan take.
Wani ganau ya ce fasinjoji 20 da lamarin ya rutsa da su sun ƙone ƙurmus har ba za a iya gane su ba.
Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, shugaban Ƙaramar Hukumar Ibarapa ta Gabas, Gbenga Obalowo, ya ce shi ne ya jagoranci tawagar ceto zuwa inda haɗarin ya afku.
alfijr Labarai
Shugaban ya jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a hatsarin.
Sai dai kuma ba a samu jin ta bakin kwamandan hukumar ta FRSC a jihar Oyo, Joshua Adekanye ba, inda bai amsa kiran waya da a ka yi masa ba.
NAN