Wani Sabon Rikici Kan Hijabi Ya Barke! Ya Janyo Rufe Wata Makaranta Boko

Alfijr

Alfijir ta rawaito a ranar Alhamis din da ta gabata ne gwamnatin jihar Kwara ta rufe makarantar Oyun Baptist High School da ke Ijagbo a karamar hukumar Oyun a jihar, sakamakon wani rikici da ya barke a makarantar.

Alfijr

Wasu mutane dauke da makamai sun yi wa daliban ta’addanci a yayin wata zanga-zangar lumana a kofar makarantar da misalin karfe 8 na safiyar ranar Alhamis.

Wani rahoto da ba a tabbatar da shi ba ya ce ana fargabar mutuwar daliba yayin da wasu kuma suka jikkata a rikicin da ya barke tsakanin Kiristoci da Musulmi kan sanya hijabi da dalibai mata musulmi suka yi.

An bayyana sunan wanda aka kashe a matsayin Habeen Mustapha.

Alfijr

Jami’an tsaro dauke da makamai wadanda aka shirya domin wanzar da zaman lafiya a yankin, sun tare babbar hanyar Osogbo zuwa Offa zuwa Ajase Ipo, tare da hana matafiya wucewa.

Jaridar PUNCH ta ruwaito rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da kakakinta Ajayi Okasanmi ya fitar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara na son sanar da jama’a musamman ‘yan kasa da mazauna yankin Ijagbo da kewaye cewa, rundunar ‘yan sanda na yau da kullum da aka tura a Ijagbo sun samu nasarar dawo da zaman lafiya, kuma suna nan a kasa domin tabbatar da tsaro, cewa ba a bar wani kara karya doka da oda ba.

Alfijr

Aikin da ke sama ya biyo bayan rikicin da ya shafi sanya hijabi a makarantu wanda al’amura ke ci gaba da ruruwa tsakanin mabiya addinin Kirista da Musulmi a jihar Kwara.

Halin da ake ciki yanzu shi ne tabarbarewar doka da sauran su tsakanin al’ummar Ijagbo da iyayen dalibai musulmi masu zanga-zangar, inda aka yi amfani da makamai ba tare da izini ba.

Alfijr

Kwamishiniyar ilimi ta jihar Sa’adatu Modibbo-Kawu, ta ce gwamnati ta yi Allah wadai da wannan aika-aika tare da sanar da rufe makarantar a wata sanarwa da sakataren yada labarai na ma’aikatar, Mista Yaqub Aliagan ya fitar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Gwamnatin jihar Kwara ta yi Allah wadai da harin da aka kai a makarantar sakandare ta Oyun Baptist mallakin gwamnati a ranar Alhamis.

Alfijr

Gwamnatin ta kara Allah-wadai da irin wannan nuna kyama da wariya ga kowa, musamman yara kan dalilan addini.

Ba za a amince da irin wannan wariyar ba a kowace cibiya mallakar gwamnati a jihar.

Yayin da gwamnati da hukumomin tsaro ke ci gaba da yin aiki da shugabanni a kowane bangare, a nan ta ba da umarnin rufe makarantar nan take har sai an warware matsalar.

Alfijr

Gwamnati ta yabawa jami’an tsaro kan matakin da suka dauka cikin gaggawa wanda ya dawo da kwanciyar hankali a yankin.

Gwamnati ta yi kira gare su da su yi bincike tare da gurfanar da duk wanda ke da alaka da tashin hankalin domin dakile wasu.

Alfijr

Ta kara kira da a kwantar da hankula saboda tashin hankali bai kawo wani abu mai kyau ba, kokarin da aka yi don jin martanin sakataren kungiyar Kiristoci ta Najeriya Rev. Reuben Ibitoye, yaci tura ya kuma kashe lambar wayarsa.