‘Yan sanda Sun Ceto Wata Mata Da Tayi Yunkurin kashe kanta

Alfijr

Alfijr ta rawaito, jami’an tsaro sashin ‘Rapid Respond Squad’ sun hana wata mata da ba a tantance ba ta kashe kanta a unguwar Iyana Oworo da ke jihar Lagos

Matar da ta yi ikirarin cewa ana azabtar da ita a gidansu, don haka ta gudu ne domin ta kashe kanta a kan gadar Third Mainland Bridge.

Alfijr

Wani ganau, ya tabbatar da ganin matar tana tafiya cikin damuwa a bakin Iyana Oworo na gadar, ya sanar da jami’an tsaro hakan.

Wani sakon da hukumar ta wallafa a Facebook ya nuna cewa jami’an sun tsare ta bayan an tserar da ita.

An kai matar zuwa ofishin ‘yan sanda ne a yayin da ake kokarin jin ta bakin ‘yan uwanta.

Alfijr

Jami’an kungiyar Rapid Response squad da ke sintiri a gadar Third Mainland Bridge suka hana wata baiwar Allah kashe kanta ta hanyar tsallake rijiya da baya.

Tana kokarin tsallewa cikin tafkin da ke wajen Iyana Oworo karshen gadar lokacin da jami’an suka tsare ta.

Matar a wata tattaunawa da ta yi da manema labarai ta bayyana cewa ‘an yi min duka a gida, shi ya sa na gudu na kashe kaina.

Alfijr

Slide Up
x