Wani Sarki ya sha da kyar yayin da ya  tsere bayan da  ƴan daba su ka kai hari a fadarsa

FB IMG 1734968256725

Wasu ‘yan daba sun kai hari fadar Etsu Nupe Lokoja, Mai Martaba Emmanuel Akamisoko Dauda-Shelika, Nyamkpa IV, a karshen mako, inda suka kona wata mota.

Alfijir Labarai ta rawaito maharan sun kai farmakin ne da misalin karfe 1.00 na daren ranar Asabar.

Yayin da yake bada labarin abin da ya faru, Etsu Lokoja, Mai Martaba Emmanuel Akamisoko Dauda-Shelika, Nyamkpa IV, ya ce harin ya zo masa ba tare da tsammani ba.

“Na ji babbar karar bugu a kofa ta, sai na farka na leka ta taga don ganin abin da ke faruwa. A lokaci guda, sai kawai na ga wuta tana ci daga motata, wanda aka kunna ta da gangan.”

“Na fahimci cewa harin fada aka yi, don haka ban fito ba saboda tsoron kada a kai min hari. Na fita ta bayan gida kuma na haye katanga domin tsira da rayuwata,” in ji shi.

Sarkin ya kara da cewa duk da kokarin da makwabta suka yi, wutar ta kone motarsa da wasu kayan da ke cikin fada.

Ya yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su gudanar da bincike kan harin tare da gurfanar da masu laifin da kuma masu daukar nauyinsu a gaban shari’a.

Daily Trust

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *