Wani Uba Da Ɗansa Sun Hadu Da Ajalinsu A Wata Rijiya A Kano

Alfijr Labarai

Alfijr ta rawaito, Wani uba mai shekaru 60, Malam Bala da dansa, Sunusi Bala mai shekaru 35, sun mutu a wata rijiya da ke Sabon Garin Bauchi, a karamar hukumar Wudil ta Jihar Kano, a lokacin da suke zubar da ruwa daga cikin ta.

Alfijr Labarai

Sanarwar da kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Alhaji Saminu Abdullahi ya fitar ta tabbatar da hakan a ranar Laraba a Kano.

Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne da safiyar Talata. Ya ce: “Mun samu kiran gaggawa daga ofishin kashe gobara ta Wudil da misalin karfe 11:30 na safe daga wani Isma’ila Idris cewa wasu mutane biyu sun makale a cikin rijiya, nan take muka aike da tawagarmu zuwa wurin da abin ya faru da misalin karfe 11:33 na safe.

An kira wani uba da dansa su yashe rijiya, sun yi nasarar yashe ta. “Amma, dan ya koma cikin rijiyar ya share ta a lokacin da ya koma sai ya makale cikinta.

Alfijr Labarai

“Mahaifinsa ya bi shi don ceto shi, lokacin da shi ma ya makale saboda rashin iskar oxygen a cikin rijiyar”.

Abdullahi ya ce. Sanarwar ta kuma ce an fito da wadanda abin ya shafa daga rijiyar a sume kuma daga baya aka tabbatar da mutuwarsu.

Ya kara da cewa an mika gawarwakinsu ga ofishin ’yan sanda model na Wudil.

Ya ce dalilin faruwar lamarin shi ne rashin iskar oxygen.

Alfijr Labarai

Kamar yadda Solacebase ta wallafa