Wasu ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Jami’an ‘Yan Sanda Da Sojoji A Shingen Binciken Ababan Hawa

Alfijr ta rawaito ‘Yan bindiga sun kai hari kan tawagar jami’an tsaro na ‘yan sanda da sojoji a wani shingen bincike a Amodu, karamar hukumar Nkanu ta Yamma, jihar Enugu.

Alfijr Labarai

Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Talata.

‘Yan bindigar sun kai hari ne a shingen binciken kan wasu motoci biyu Lexus RX SUV da Toyota Sienna guda daya sannan suka bude wuta kan jami’an tsaro.

Sai dai jami’an tsaron sun yi kokari matuka inda suka sami nasarar dakile harin.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Enugu, Daniel Ndukwe, ya ce a halin yanzu jami’an tsaro na nan suna binciken in da maharan suka boye.

Alfijr Labarai

“An kai hari a wani shingen binciken jami’an hadin gwiwa da ke Amodu a karamar hukumar Nkanu ta Yamma, da safiyar yau 27/09/2022,” inji shi.

“Duk da haka, ina jiran cikakken bayani kan lamarin, domin fadada farautar maharan da suka rufe fuska, wadanda akasarinsu sun tsere daga wurin da lamarin ya faru da munanan raunukan harbin bindiga, bayan fafatawar da suka yi da rundunar.

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *