Daga Rabi’u Usman
Mai shari’ah Simon amobede na babbar kotun tarayya mai lamba 3 dake zaman ta a nan kano ya bayar da Belin Hajiya Rabi Lawan mai kamfanin Anadariya traveling agency bisa sharuddai 6.
Alfijir labarai ta rawaito sharadi na farko, mutane 2 zasu tsaya mata akan N20m kowannen su, sharadi na biyu, su kasance yan uwanta ne na jini, sharadi na uku, su bayyana shaidar mallakar gida ko fili mai dauke da shaidar mallaka ta gwamnati C.of.O. sharadi na hudu, zasu bayar da takardun shaidar biyan kudaden haraji ga gwamnatin tarayya na tsawon shekaru 3, sharadi na 5, Rabi zata ajiye dukkannin takardun shaidar fita kasashen ketare da passport dinta, a karshe Rabi Lawan zata dinga zuwa kotu duk zaman da za’ayi, idan kuma ta karya daya daga cikin wadannan sharuddai kotun zata karya belin ta data bayar.
Tunda fari dai, Wasu mutane daga sassa daban daban a jihar kano da wasu jihohin suka kulla alakar kai mutane kasashen ketare domin yin aikin kamfani da aikace aikace, mutanen sun shigar da karar ne domin neman hakkin su a wajen Hajiya Rabi Lawan Zunzurutun Kudi sama da Naira Miliyan dari 2.
Tun a baya, an karantowa Rabi kunshin tuhumar da ake yi mata, amma ta musanta, saidai lauyan Rabi Lawan Barr Abdullahi Alhassan Usman ya Nemi a bayar da belin ta.
A zaman kotun na yau, kotu tayi kwarya kwaryar hukunci inda ta bayar da belin ta, sannan kotun ta sanya ranar 23 ga watan janairu na shekarar 2025 domin cigaba da Shari’ar.
Bayan fitowa daga kotun wakilin mu ya zanta da Barr Nura A Sa’id inda yace, “sun gamsu da yanda wannan shari’a ke tafiya”
A nasa bangaren lauya me kare Hajiya Rabi a wannan shari’a Barr Abdullahi Alhassan Usman Wanda ya gabatar da suna A.U Alhassan a gaban kotun, yace ba zaice komai akan wannan shari’a ba.
Hakan ne tasa muka zanta da wadanda suke neman hakkin su a wajen Hajiya Rabi, inda sukayi fatan kotu zata kwato musu hakkin su.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj