Wata Kotu Ta Aike Da Wani Mutum Gidan Gyaran Hali Kan Satar Dunkulen Girki A Kano

Alfijr

Alfijr ta rawaito mai shari’a alkali Dokta Bello Khalid na Kotun Shari’ar Musulunci, ya bayar da umarnin tisa keyar matashin zuwa gudan gyaran hali a jihar Kano, hakan ya faru ne bayan an gurfanar da matashin kan zargin sace kwali 22 na dunkulen dandanon girki

Da yake karanta tuhumar Insfekta, ya ce ana tuhumar matashin ne da aikata sata da kuma cin amana bayan wani mai suna Jamilu Ibrahim mazaunin unguwar Galandanci ya kai karar shi a ofishin ’yan sanda na Sabon Gari a ranar 10 ga watan Maris.

Insfekta Wada ya shaida wa kotun cewa Jamilu ya ba wa wanda ake zargin kwali 260 na dunkulen dandanon girki ya ajiye a shagonsa.

Alfijr

Amma da Jamilu ya je karbar kayan sai ya iske kwali 22 na dunkulen dandanon —wadanda kudinsu ya kai N216,000 — sun yi layar zana, sai dai matashin da ake zargi, mai shekara 37, ya musanta laifin da ake tuhumar shi da aikatawa.

Daga nan ne, Mai Shari’a Dokta Bello Khalid, ya ba da umarnin a tsare shi a gidan yari, sannan ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 8 ga watan Afrilu. 2022