Wata Kotun shari’ar Musulunci A Kano Ta Aike Da Wani Matashi Aminu Suraj Gidan Gyaran Hali

Alfijr ta rawaito wata kotun shari’ar Musulunci da ke zamanta a unguwar Fagge dake birnin Kano a ranar Laraba, ta bayar da umarnin tsare wani yaro dan shekara 18 mai suna Aminu Surajo da ya amsa laifin satar kwanan rufin da ya kai Naira 6,000 a gidan gyaran hali da tarbiyya

Wanda ake zargin yana zaune a unguwar Sheka Tsamiya da ke Yankifi a karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano.

Ana tuhumar Aminu Suraj da laifuka biyu da suka hada da aikata laifuka da kuma sata, ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.

Alfijr

Alkalin kotun, Ismail Muhammed Ahmad ya bayar da umarnin a tasa keyar wadanda ake zargin a gidan gyaran hali, ya kuma dage sauraron karar zuwa ranar 15 ga watan Yuni domin yanke masa hukunci.

Tun da farko dai lauyan masu shigar da kara, Abdul Wada, ya sanar da kotun cewa wanda ake tuhumar ya aikata laifin ne a ranar 8 ga watan Mayu a Sheka Gidan Leda.

Alfijr

Ya ce da misalin karfe 10:15 na dare wanda ake kara ya kutsa cikin gidan wani Jamilu Idris da ke Sheka Gidan Leda Quarters, Kano.

Wada ya ce wanda ake tuhumar ya kwashe rufin Idris, Wada ya ce laifin ya ci karo da tanadin sashe na 133 na dokar shari’ar jihar Kano.

Slide Up
x