Alfijr ta rawaito a wani babban taron jam’iyyar APC a Kano ranar Litinin ya rikide zuwa bawa hammata iska, yayin da shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai Alhassan Doguwa ya kaiwa mataimakin dan takarar Gwamna na jam’iyyar Murtala Garo mahangurba.
Alfijr Labarai
Taron wanda aka gudanar a gidan
mataimakin gwamna Nasir Gawuna, an
shirya shi ne domin duba nasarori da
gazawar da aka samu a ziyarar dan takarar
shugaban kasa na jam’iyyar, Bola Tinubu.
Daily Nigerians ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a lokacin da Alhassan Doguwa, wanda ba a gayyace shi taron ba, ya je
ganin shugaban jam’iyyar, Abdullahi Abbas. Wani mai magana da yawunsa ya shaidawa
Daily Nigerian cewa, da isar shi wurin taron, Doguwa ya fara korafin cewa shugabannin jam’iyyar sun mayar da shi
saniyar ware kan al’amuran da suka shafi kudi a jam’iyyar, amma sai kawai aka gayyace shi don aiwatar da ayyuka masu wahala.
Alfijr Labarai
“Alhassan Doguwa ya fara afkawa
mataimakin gwamna Gawuna da bakaken maganganu kafin ya juya ga Murtala Garo.
Ya yi korafin cewa Murtala ya umurci yaran sa na siyasa da su rufe hotonsa a fastocin
da aka buga yayin ziyarar da Tinubu ya kai jihar Kano, alhalin a gaskiya Murtala ba shi
da hannu a hakan,” inji wata majiya.
Majiyar ta ƙara da cewa a kokarin da ya yi na dakile harin da hannunsa, tarkacen
kofin gilashin ya bugi Garo a
hannunsa kuma ya raunata shi.
Sai dai taron ya tashi ne bayan faruwar lamarin, inda mataimakin gwamnan ya gargadi Doguwa da ya fita daga gidan sa.
Alfijr Labarai
Kafin faruwar lamarin a ranar Litinin din da ta gabata, Daily Nigerian ta bayyana cewa Doguwa ya zargi kwamishinan yada labarai na jihar, Mohammad Garba, Kan kin sanya sunansa a cikin jadawalin jawabai a lokacin kaddamar da littafin
Gwamna Abdullahi Ganduje na kwanan nan
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb
Alhammudlillah”‘Alhammudlillah
Hahahhaaha
D