Wata Sabuwa! Sarki Ali Nuhu Ya Maka Jaruma Hannatu Bashir Gaban Kuliya

Hakazalika alfijr ta waiwayi Jaruma Hannatu kan zargin da Ali ke mata wanda har ya bashi damar garzayawa Kotu don neman hakkinsa, duba da ga dattijai a masanatar amma ya tsallake su?

Alfijr Labarai

Hannatu tace, wannan shi ake cewa girma ya faɗi Rakumi ya shan ye ruwan ƴan tsaki, wato dai borin kunya ne kawai irin na Ali, ya zalinceni ya sakani asara amma tunaninsa ni zan kai shi karar shine shi kuma yayi kankaga biri, wato yayi jiga malam masallaci ya kaini.

Jarumar ta ce, babu komai tsakanina shi sai girmama da darajawa, amma ya amince da ranar da ya zaba da kansa da zummar za muyi wani aiki dashi, da lokacin ya zo mun riga mun biya kudin wajen bayan Ƙara amincewarsa ta halartar aikin sai ya ki zuwa.

Bayan da muka Ƙara tuntubarsa a karo na gaba, sai ya ce tafiya ce ta kama shi, amma a ranar zai biyo jirgin yamma ya dira, idan ya so gobe sai a dora inda aka tsaya.

Alfijr Labarai

Washegari muka tuntubi Ali sai ya sake ce mana shi fa bai taso ba sai ranar da yamma, kuma idan yazo gida zai wuce abinsa ya huta sai kuma gobe.

To wannan shine abin da ya fara faruwa tsakanina da shi, kuma duk ba da ni suke maganar ba sai da wakilina, wato Alolo.

Idan wanda baya masana’antar bai san menene fim ba to shi Alinfa?

Wannan kwana biyu da yaki zuwa ba karamar asara ya jawo mana ba kuma yasan haka, wannan tasa na tura masa sakon karta kwana kan jashin jin daɗin abinda yayi mana a matsayinsa na babba! In ji Hannatu

Alfijr Labarai

Ta kara da cewa, wannan abinda na aika masa shine wai nayi masa rashin kunya sai ya kaini ga hukuma.

Fatanmu anan shine a sami fahimtar juna da dai dai to, duba da yan gida ɗaya ne, kuma ga manya a gidan, kamata yayi ko menene ayi shi a gida a gama wani ma bai ji ba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *