Wata Sabuwa! Wutar Lantarkin Najeriya Ta Sake Dauƙewa Gaba Ɗaya A Faɗin Kasar Karo Na 4

Screenshot 20240706 200536 WhatsAppBusiness

Daga Aminu Bala Madobi

Wutar lantarki ta dauƙe gaba ɗaya a faɗin Najeriya sakamakon durƙushewar babban layin lantarkin ƙasar.

Alfijir labarai ta ruwaito wutar lantarkin ta sake ɗaukewa gaba ɗaya ne, bayan da ta ragu zuwa 0.80 a ranar Asabar.

Binciken da aka yi a shafin intanet na kamfanin da ke kula da wutar lantarkin ya nuna yadda ya fara raguwa da misalin ƙarfe 2 na rana zuwa megawat 2,797.16.

Ƙarfin wutar lantarki ya ƙara raguwa zuwa 1,020.08 da misalin ƙarfe 3 na rana kafin ya ƙasa sosai zuwa 0.80 da misalin ƙarfe 4 na yamma.

Rahotanni na nuni da cewa ta ruwaito cewa 0.80 shi adadin abin da babban layin samar da wutar lantarki ke da shi a yanzu haka.

Wannan shi ne karo na huɗu da babbar tashar samar da wutar lantarki ta Najeriya ke faɗuwa a 2024.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *