Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) ta fitar da cikakken jadawalin rukuni na gasar cin Kofin Duniya ta shekarar 2026 a wani babban taro da ta gudanar a birnin Washington D.C na Amurka.
Gasar, wadda za a yi a ƙasashen Mexico, da Kanada da Amurka daga 11 ga Yuni zuwa 19 ga Yuli, za ta kasance gasar farko da za ta ƙunshi ƙasashe 48, abin da zai ƙara yawan wasanni da tsananin gogayya.
Sabon tsarin ya haifar da rukuni 12, inda kowanne rukuni ya ƙunshi ƙasashe huɗu. Brazil, wadda ta fi lashe gasar a tarihi, na rukunin C tare da Morocco, Scotland da Haiti. A gefe guda kuma, Ingila ta shiga rukunin L, inda za ta fafata da Croatia, Panama da Ghana.
Wasu manyan fafatawa da ake sa ran zasu ja hankali sun haɗa da Amurka a gida a rukunin D tare da Australia da Paraguay, sai kuma Spain a rukunin H tare da Uruguay, Saudi Arabia da Cape Verde.
Hukumar ta ce sabon tsarin ya ba da damar ganin ƙasashe masu tasowa da waɗanda suka fi ƙarfi suna haɗuwa a matakin rukuni, domin samar da sabbin ƙalubale a gasar.
Haka kuma, an bar wasu gurabe domin ƙasashen da za su fito daga wasan share fage na Turai da sauran yankuna, wanda hakan ke ƙara jan hankali kan yadda jadawalin ƙarshe zai kammala.
Ga cikakken rukuni 12 kamar yadda FIFA ta fitar:
A: Mexico, Koriya ta Kudu, Afirka ta Kudu, (mai yiwuwa Jamhuriyar Ireland)
B: Canada, Switzerland, Qatar, (Wales ko Northern Ireland)
C: Brazil, Morocco, Scotland, Haiti
D: Amurka, Australia, Paraguay, (wanda ya lashe share fage na Turai)
E: Jamus, Ecuador, Cote D’Ivoire, Curacao
F: Netherlands, Japan, Tunisia, (wanda ya lashe share fage na Turai)
G: Belgium, Iran, Masar, New Zealand
H: Spain, Uruguay, Saudi Arabia, Cape Verde
I: Faransa, Senegal, Norway, (wanda ya lashe share fage)
J: Argentina, Austria, Algeria, Jordan
K: Portugal, Colombia, Uzbekistan, (wanda ya lashe share fage)
L: Ingila, Croatia, Panama, Ghana
Gasar ta bana za ta ƙara faɗaɗa tarihi, domin ƙaruwa daga ƙasashe 32 zuwa 48 na nufin ƙarin dama ga ƙasashe da dama da kuma tsananin gogayya tun daga rukuni har zuwa zagaye na gaba.

Leadership
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t