Ta Sake Faruwa: Babban layin wutar lantarki na ƙasa ya katse

FB IMG 1767034266504

An samu katsewar wutar lantarki a sassa da dama na Najeriya a ranar Litinin bayan babban layin wutar lantarki na ƙasa ya faɗi, lamarin da ya jefa miliyoyin mutane cikin duhu.

Bayanan Hukumar NISO sun nuna cewa samar da wuta ya fadi daga megawatt 2,052 zuwa kasa da megawatt 140 cikin awa guda.

Kamfanonin rarraba wuta uku kacal—Ibadan, Abuja da Benin—ne suka samu wuta, yayin da sauran kamfanoni basu samu ba.

Katsewar ta tilasta wa gidaje, ’yan kasuwa da cibiyoyi dogaro da janareto.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, TCN da NERC ba su fitar da sanarwa kan dalilin katsewar ba ko lokacin dawo da wutar ba.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *