YADDA AKE FITAR DA NISABI A TSARIN ADDININ MUSULUNCI

Alfijr

Alfijr Labarai na muku barka da Juma a da fatan alheri ameen.

YADDA AKE FITAR DA NISABI


A wannan lokacin Giram din Gwal ďaya (1) ana sayar da shi N27,000:00 Giram 4.25 shi ne yake bayar da nauyin cikakken Dinare
na asali dan Madina.

Dinare Ashirin (20) shi ne Nisabin Zakka wanda yake dauke da nauyin Giram 85 na ma’aunin zamani
(sikeli).

Alfijr

A don haka farashin Giram 4.25 na ma’aunin zamani shi ne a matsayin farashin Dinare ďaya (1).

Ta haka ne za a fitar da
Nisabi a kowane lokaci, domin farashin Gwal yana hawa da sauka. Allah ya sa mu dace

Kamar yadda hukumar Shari ah ta jihar Kano muke fito dashi duk shekara don anfanin al ummar Musulunci.