Alfijr
Alfijr ta rawaito hukumar Shari ah ta jihar Kano ta rawaito yadda nusabin zakka, sadaki da diyyar rai yake ta bana kamar yadda ta saba duk shekara.
MAFI KARANCIN SADAKI
₦28,687.50 shine mafi karanci, amma mutum zai iya bada sama da haka bisa kyautatawarsa.
Kuma wannan kaso wato, ₦28,687.50 shi ne kimar da za a yanke hannu a idan mutum yayi sata.
NISABIN ZAKKA ZAI FARA DAGA ₦2,295,000.00
Za a kasa wannan kucin gida (40) wanda zai zaino ₦57,375.00 shi za a bayar
Idan kudin ya haura Nisabi, za a kasa gida Arba’in (40) a bayar da kashi daya (1/40)
Alfijr
Diyyar Rai A MUSULUNCI : ₦114,750,000.00
Wannan kimar nisabin zai iya sauyawa daga lokaci zuwa lokaci,
sakamakon hawa da saukar Dinare
NISABIN ZAKKAR DABBOBI
RAKUMA
Daga (5 – 9) Akuya 1
Daga (10 – 14) Awaki 2.
Daga (15 – 19) Awaki 3
Daga (20 – 24) Awaki 4.
Daga (25) abin da yai sama za a fitar daga Rakuma.
Alfijr
SHANU: Daga (30) za a ba da Maraki
AWAKI/TUMAKI: Daga (40-120) za a ba da
Akuya/Tunkiya. Idan suka kai dari da ashirin da daya sai a ba da biyu har zuwa
dari biyu da daya sai a ba da uku, daga nan kowace dari za a ba da daya.
NISABIN ZAKKAR AMFANIN GONA
Abin da ya kai kwano (300) wanda yake daidai da wusiki 5, za a fitar da kashi daya bisa goma (1/10) na noman ruwan sama, kwano (30).
Abin da ya kai
kwano (300) wanda yake daidai da wusiki 5, za a fitar da kashi daya bisa
ashirin (1/20) na noman rani, kwano (15).
Alfijr
Don neman Karin bayani a iya kiran wannan lambar.
08028494926