Mun Cuci Najeriya! Ya kamata Buhari Ya Daure Ni Da Sauran Yan Siyasa! Inji Ibrahim Musa Kazaure

Alfijr ta rawaito tsohon Ministan ayyuka , Ambasada Ibrahim Musa Kazaure ya ce ya kamata Shugaba Muhammadu Buhari ya kama shi da sauran ƴan siyasa da su ka rike madafun iko a ɗaure su sabo da sun zalunci ƙasar nan.

Ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da shi a Radio France International, cikin wani shiri

Kazaure ya ce duk ƴan siyasar Najeriya ɗaya su ke, babu wani wanda ya ke yi don talakawa, na kuma shaidawa Shugaba Buhari da ya kame duk ƴan siyasar da su ka wawashe kuɗaɗen gwamnati har da ni, domin mun zalunci ƙasar nan.

Alfijr

Tsohon Ministan ya ce duk ƴan siyasan da su ka rike madafun iko tun daga 1999 ba su yi wa ƙasar komai ba.

“Har ni da na ke wannan maganar, ya kamata a ɗaure mu sabo da ba mu yi wa ƙasar nan komai ba, na sha faɗin cewa ni Ibrahim Musa Kazaure, mun zalunci Najeriya da talakawanta.

Alfijr

“Magana ta gaskiya ita ce, dukkan yan siyasa kanwar ja ce. Abin da mu ka yi wa Najeriya ba haka ya dace mu yi mata ba sabo da wasu daga cikin mu sun samu dama wasu kuma basu samu ba.

“Ni dai gaskiya na faɗa, dukkkan mu da mu ka yi sata, a matsemu mu dawo da kuɗaɗen da mu ka sata, na faɗawa Buhari, a kame mu a ɗaure mu har sai mun dawo da kuɗaɗen da mu ka sata.

Alfijr

“Ni ba zan sake karɓar wani muƙami a kasar nan ba, ko da kyauta ne,” in ji Kazaure.

Slide Up
x