Alfijr ta rawaito Kungiyar kwadago ta Najeriya reshen Kano da sauran kungiyoyi sun gaza cimma matsaya da gwamnatin jihar Kano kan tsarin biyan albashin ma’aikatan jihar na watan Fabrairu.
Alfijr
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin jihar ke kokarin biyan ma’aikatanta albashin watan Fabreru sakamakon cire kudaden da FAAC ke bai wa Jihohi.
Kungiyar ta NLC reshen jihar, Kwamared Ado Minjibir a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Alhamis, ya ce bayan wani taro da aka yi tsakanin majalisar sa, da sauran masu ruwa da tsaki irin su TUC JNC, kungiyar ’yan fansho ta Najeriya da kuma shugaban ma’aikatan jihar da Barr Binta Ahmad.
Alfijr
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa ba za ta iya biyan mafi karancin albashi na 30,000 na watan Fabrairu ba saboda raguwar kason da aka yi mata, a sakamakon haka ta ba da shawarar yin amfani da tsarin albashi na Afrilu 2021 inda aka cire wasu kaso daga ma’aikata jihar yayin da aka biya ma’aikatan kananan hukumomi mafi karancin albashi 18,000.
“An gayyace mu taron da gwamnatin jihar a ranar Talata ta hannun shugabar ma’aikata ta jihar, inda shugabar ma’aikata Barista Binta Ahmad ta sanar da mu cewa gwamnatin jihar ba za ta iya biyan mafi karancin albashi na 30,000 ba a sakamakon haka, kudaden da aka samu daga rabon FAAC”.
Alfijr
A cewarsa,Barr Binta ta bayyana cewa ” an raba zunzurutun kudi har naira biliyan dari biyar da arba’in da hudu (N500,44,000,000, 000) a fadin jihohin tarayyar kasar nan a watan Janairun 2022 sabanin naira biliyan dari shida da casa’in da tara (N699). ,000,000, 000) wanda aka raba don watan Disamba 2021, wurin biyan ma’aikata albashin Afrilu 2021
Minjibir ya bayyana cewa idan har aka yi wannan biyan, to babu shakka, za a samu raguwar kudaden da ake aikawa da amintattun asusun fansho na jihar Kano, sannan kuma za a rage biyan kudaden fansho na wata-wata.
Alfijr
Bayan haka, mun gana da dukkan shugabannin sassan gwamnati daban-daban na jihar kan ci gaban da aka samu da nufin tuntubar juna a kan lamarin mu da gwamnati.
Mun koma ga gwamnati da shawarwari guda uku da suka hada da; da farko dai jihar ta ci gaba da biyan albashin watan Afrilu na 2021 amma tare da yarjejeniyar da bangarorin biyu suka rattabawa hannu kan cewa a biya ma’aikata bambancin albashin watan Maris na 2022 idan rabon FAAC ya kai naira biliyan 700.
Alfijr
Na biyu kuma mun ba da shawarar a kafa kwamitin hadin gwiwa tsakanin Gwamnatin Jiha da ’Yan kwadago da za su je nemo gaskiya daga jihohin da ke makwabtaka da Kaduna da Jigawa da Bauchi da Sakkwato don gano yadda za su bi wajen kara biyan albashi.
karancin rabon FAAC ne a fadin kasar nan domin ba mu taba jin daga wadannan jahohin an rage albashin ma’aikata ba.
Alfijr
Na uku, wannan gwamnati ta kara himma kan kudaden shiga da ake samu a cikin gida tare da kokarin kaucewa duk wani zagon kasa, ta yadda za a iya amfani da rarar kudin wajen kara duk wani gibi na biyan albashi daga yanzu kuma ya kamata gwamnati ta yi watsi da al’adar adana irin wadannan kudaden na iya taimakawa halin da ake ciki kamar haka da kuma wajen biyan fensho.
Amma kash! Sun amince da shawarwarin na biyu da na uku amma sun ki amincewa da na farko wanda ya ce kudaden da aka cire daga albashin ma’aikata za a biya su daga baya tunda FAAC ma ba za ta biya su ba.
Alfijr
A bisa ga wadannan muna sanar da daukacin ma’aikatan jihar da sauran jama’a cewa kungiyar NLC da sauran shugabannin kungiyoyin kwadago na jihar sun nesanta kanmu daga wannan shawarar, mun rubuta wa kungiyar ta kasa wasika tare da kira ga dukkan ma’aikata da Ku kwantar da hankalinmu yayin da muke jiran karin umarni. Inji camarade Ado Minjibir
Kamar yadda jaridar Metro Daily Nigeria ta rawaito