Innalillahi wa inna ilaihirraji un! Karamin Yaro Ya Fada Rijiya Garin Rainonsa A Kano

Alfijr

 Rijiyar da ta ci mutum hudu
Gaba Dubu

Alfijr ta rawaito wani karamin yaro mai wata 19 ya fada a rijiya a gidan da aka kai shi raino a Karamar Hukumar Dambata ta Jihar Kano.

Wani ganau ya shaida wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne bayan kakar yaron da aka kai wa rainon shi ta bar shi ya yi wasa a farfajiyar gida shi kadai, iyayensa yaron sun kai shi raino ne a wajen kakarsa da ke zaune a Dambatta.

Alfijr

A nasa bangaren kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Alh Saminu Abdullahi, ya ce hukumar ta samu kiran neman agaji daga wani mai suna Salisu Bello, nan take suka tura jami’ansu zuwa wurin don ceto yaron.

Bayan an shiga rijiyar don ceto yaro, an samu ya riga ya rasu sakamakon shan ruwa da ya yi a cikin rijiyar.

Alfijr

Kakakin kwana kwana, sun ciro gawarsa daga rijiyar kuma sun fara bincike kan abin da ya faru,” amma tuni aka mika gawar ga kakan mamacin, Malam Abdulkadir don yi masa sutura.

Ya kuma ja hankalin iyaye da su kasance masu lura da yaransu don gujewa faruwar irin hakan.

Alfijr

Kamar yadda Aminiya ta rawaito.

Slide Up
x