Majalisar dokokin jihar Kano ta ce ta kuduri aniyar tabbatar da ingantattun tsare-tsare na walwala ga ma’aikatan Hisba domin tabbatar da samar da ayyuka masu inganci.
Alfijir labarai ta rawaito mamba mai wakiltar mazabar Minjibir, Alhaji Abdulhamid Abdul ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin mataimakin babban kwamandan hukumar Hisba ta jihar Kano Dr Mujahideen Aminuddeen Abubakar a harabar majalisar da ke Kano.
Gwamnatin jihar ta kafa hukumar Hisbah ta jihar Kano a shekarar 2000 kuma an ingantata a shekarar 2003 tare da samar da jami’an tsaro na Hisbah.
Tun da farko Abdulhamid Minjibir ya dauki nauyin kudirin doka da ke kira ga sake duba albashi da alawus-alawus na Hukumar Hisba don shiga cikin ma’aikatan gwamnati.
Ya bayyana cewa saboda rawar da kwamitin ke takawa majalisar za ta duba batun gyaran dokar kafa hukumar Hisbah domin amincewar bangaren zartarwa daga baya.
“An gabatar da kudirin kuma an amince da shi kafin mika shi ga bangaren zartarwa za mu bi diddigin aiwatar da shi insha Allah”
Mataimakin Kwamanda, Dr Mujahideen Aminuddeen Abubakar ya yabawa mamba mai wakiltan Minjibir bisa hangen nesa wajen daukar nauyin kudirin.
Ya yi nuni da cewa hukumar Hisbah ta jihar Kano ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kokarin tsaftace Kano daga duk wani nau’i na munanan dabi’u.
Idan za a tuna a ranar Litinin 14 ga watan Oktoba 2024 memba mai wakiltar Minjibir Abdulhamid Abdul ke gabatar da kudirin yin kira ga majalisar dokokin jihar Kano da ta duba yiwuwar sake shigar da jami’an Hisbah cikin ma’aikatan jihar baya ga sake duba sunayensu da alawus-alawus.
RN
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj