Yadda Yan Sanda Suka Kamani, Ba Tare Da Sanin Cewar Nine Kwamishinan Ƴan Sanda Ba – In Ji MD Abubakar

FB IMG 1754677377573

“A lokacin da nake Kwamishinan Ƴan Sanda a jihar Lagos, bana wasa da aiki — musamman ranar Asabar. Ko da yake ayyuka na suna farawa ne daga karfe 10 na safe, wannan rana na tashi tun 6 na safe don in kai ziyara ba tare da sanarwa ba.

Na hau motata Jeep na nufi ofis, amma sai na yanke shawarar yin ‘yin ziyarar ba-zata’ ga wasu ‘yan sanda a kan hanya – domin in ga irin yadda suke gudanar da aikinsu.

A wani shingen bincike “checkpoint” dake titin Herbert Macaulay, wasu matasan ‘yan sanda suka tsaida ni. Wani karamin dan sanda (constable) ya kalle ni yace:

> “Kai saurayi, ina zaka ne da motar mahaifinka?”

Ya bukaci takardun motar da shaidar lasisin tuƙi. Na ce masa sunana Mohammed. Yace dole sai na nuna ID card. Na ce masa, to ya fara nuna mini nasa. Bai da ID card, don haka sai ya kira sergeant dinsu.

Shi ma sergeant din ya bukaci ID card dina, na ce masa ya nuna mini nasa kafin nawa. Ganin bana jin tsoro ko nuna daraja, sai suka ce mu tafi ofishin ‘yan sanda na Yaba (Panti) domin “gano ko ni wanene”.

Muna isa station – babu parking sai a wajen DPO. Na ajiye motata a can, constable din ya fusata yace: “Wannan wajen parking din DPO ne fa!” Ko uffan ban ce masa ba.

Bayan mun shiga ciki, sai suka kaini wurin wani ASP (Assistant Superintendent of Police) wanda ke sanye da gajeren wando ‘shorts’!. Yace na shigo, na ki, nace masa ba zai yiwu ya tuhumeni cikin kayan gida ba. Yayi fushi ya jawo ni ciki da ƙarfi – nima ina jan shi. Da ya duba fuskata da kyau sai ya fara zare ido…

A gefe guda, wani tsoho da ke ofishin ya leƙa ofishin DPO don duba hoton shugabannin rundunar Ƴan sanda dake jikin bango. Da ya tabbatar cewa ni ne, sai kawai ya tsallake taga ya gudu!

Sergeant da ya kawo ni ya kasa gane me ke faruwa, har sai da wani Ɗan sanda ya matso kusa da kunnensa, ya ce masa: “Kai, CP ne wannan fa!”

Cikin firgici, ASP ɗin da ke sanye da shorts ma ya bi taga ya gudu!

Bayan haka, Area Commander ya kirani ya tambaya me ya faru. Aka gaya masa cewa an tsare DPO, ASP, da sauran ‘yan sanda da suka shiga lamarin – suna jiran umarni na.

Abin da ya fi tada min hankali ba wai kamun da suka yi min ba ne – a’a, amma irin yadda suka nuna rashin tarbiyya, rashin horo, da rashin kwarewa a aiki

Yaya dan sanda zai tsaya a titi ba tare da ID ba, yana tsare jama’a? Yaya ASP zai zauna da kaya irin na gida yana sarrafa aiki? Wannan ya kara tabbatar min da cewa shugabanci ba sai ka zauna ofis ba – dole ka fita ka duba, ka gani da idonka, ka tabbatar da gaskiya da adalci a kowanne mataki

Fassara: AB Damare

Arewa Post

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *