Yadda ziyarar kungiyar AROGMA zuwa Cibiyar Hada-Hadar Cinikayyar ta Kamfanin Dangote ta haifar da alheri

IMG 083423 23925 1758612901452

…Mun zo ne don yabawa kan kokarin da kamfanin ke yi na gabatar da ayyukan jin kai da kuma jigilar man fetur kyauta a kokarin saukaka tsadar farashin ga talakawan Najeriya

Kungiyar dillalan man fetur da iskar gas ta Arewacin Najeriya (AROGMA) da ayarin mahukunta sun kai ziyarar ban girma zuwa Cibiyar Hada-Hada da tallace tallace ta matatar Dangote a ofishin su dake birnin Kano a karshen makon daya gabata.

Masu ruwa da tsaki na Kungiyar dillalan man fetur da Iskar gas na Arewacin Najeriya sun yaba wa kwazo da hangen nesan shugaban rukunin Kamfanonin Dangote da tawagarsa ‘yan kishin kasa bisa ayyukan su na sadaukarwar da suka yi wajen ceto al’ummar Najeriya daga durkushewar tattalin arziki da ke gabatowa.

Yayin ziyarar, Kungiyar sun cimma matsaya wajen ganin an ceto al’ummar kasar daga matsalar makamashi da kuma kawo ƙarshen karancin man a kasashen waje ta hanyar kawo karshen dogaron da kasar ke yi na shigo da albarkatun mai.

Cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar dillalan mai da iskar gas ta Arewacin Najeriya Alh Bashir Ahmad Danmalam ya fitar bayan ganawa da Hajiya Halima Dangote da Jami’in gudanarwa Malam Garba

Danmalam ya bayyana cewa, shugabancin kungiyar AROGMA, ya yabawa Halima Dangote, da kuma Malam Garba, wanda ya wakilci matatar Dangote, bisa kokarinsu, da kuma hangen nesan su kan yadda za a rika dora man fetur ga ‘yan kungiyar AROGMA, kuma sun amince da yin rajistar lodin man za a dinga yi musu kyauta a yanzu.

Ya kara da cewa a yayin taron, AROGMA ta gabatar da kalubalen da ke gabanta da kuma nasarorin da za a iya samu yayin da ake shirye-shiryen fara lodi daga matatar Dangote.

Shugabancin daganan ya nemi karin haske daga wajen Hajiya Halima kan hanyar da za a bi, inda ta ba su shawarwari kan yadda za su kulla huldar kasuwanci da matatar kai tsaye. 

A cewar Dan mallam dukkan ‘yan kungiyar AROGMA za su ci gajiyar lodin man fetur, inda kuma a halin yanzu rijistar kyauta ne. 

Ya tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba ‘yan kungiyar AROGMA za su fara lodin man fetur tare da rarraba shi.

“Wannan babbar dama kuma babbar nasara ce, kuma muna kira ga membobinmu da su yi amfani da wannan dama, kasancewar akwai romo sosai,” in ji Danmalam. 

A karshe ya ce wannan damar ba wai kawai mambobin kungiyar ta AROGMA za su amfana ba har ma da masu amfani da su da kuma daukacin al’ummar Najeriya.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *