Gwamnan Kano ya sauyawa wasu kwamishinoni da ma’aikata gwamnati wajen aiki

FB IMG 1753107424455

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da sauyawa wasu kwamishinoni ma’aikatu, sannan kuma an sauyawa wasu ma’aikatan gwamnati a wasu muhimman ma’aikatun jihar.

Wannan na kunshe ne a cikin sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature, ya aikowa  manema labarai a jiya Litinin.

Ya ce matakin yana daga cikin kokarin gwamnati na kara karfafa shugabanci da inganta ayyukan gwamnati a fannoni daban-daban.

A cewar sanarwar, Kwamishinan Shari’a na jihar, Barista Haruna Isa Dederi, an mayar da shi zuwa Ma’aikatar Sufuri. Haka kuma,  Darakta a Ma’aikatar Shari’a, Barista Mustapha Nuruddeen Muhammad, an mayar da shi Ma’aikatar Muhalli a matsayin Babban Sakatare.

Kwamishinan Harkokin Jin Kai, wanda ya kasance mai rikon kwarya a Ma’aikatar Sufuri, zai koma ma’aikatarsa ta asali, wato ta Harkokin Jin Kai.

Gwamnan ya umurci dukkan jami’an da sauye-sauyen suka shafa da su mika ragamar ofisoshinsu ga manyan jami’an da ke cikin ma’aikatun kafin kammala aiki gobe Talata, 23 ga Satumba, 2025.

Gwamnan ya jaddada kudirin gwamnatinsa na gaskiya, inganci da shugabanci nagari, tare da bukatar jami’an gwamnati su ba da hadin kai ga sabbin kwamishinonin domin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *