Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta tsare wata mace mai suna Zuwaira Hassan da zargin yi wa yarinya mai shekara 10 azaba da wuta a gabanta bayan saka cokali a wuta.
Kakakin rundunar, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya faɗa cikin wata sanarwa jiya Juma’a cewa matar ta bayyana musu cewa ita da ‘ya’yanta maza biyu ne suka aikata hakan.
A cewar sanarwar: “Zuwaira ta ce a ranar 8 ga watan Satumba da misalin ƙarfe 11:00 na dare ne yarinyar ta faɗa mata cewa ɗakin da suke ciki ita da ‘ya’yanta zai rushe kuma ya kamata su sauya wurin kwana. Sannan ‘ya’yan nata suka faɗa mata yadda suke yin mummunan mafarki da yarinyar.
“Bisa wannan dalilin ne wadda ake zargin [Zuwaira] ta kai ‘ya’yan nata wajen wata mai maganin gargajiya Fatima Abdullahi, wadda ta ce yarinyar mayya ce, kuma ta bai wa wadda ake zargi magungunan kariya.
“Bayan haka ne matar ta saka cokali a wuta, ta umarci ‘ya’yanta Umar Ibrahim da Abubakar Ibrahim su ɗaure hannaye da ƙafafuwan yarinyar, sannan ta saka cokalin mai zafi a gaban yarinyar a matsayin hukunci, tana mai cewa mai maganin ce ta umarce ta da yin hakan.
“Mai maganin ta buƙaci Zuwaira ta biya ta naira 150,000 kuɗin maganin, amma suka daddale kan naira 40,000, inda aka ba ta maganin wanka da kuma na hayaƙi.”
CSP Wakil ya ce dakarunsu sun kai yarinyar Babban Asibitin Toro domin kula da lafiyarta, kuma suna tsare da mai maganin ita ma.
BBC
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t