Da Sauran Rina A Kaba! Bayan Kulle Wasu Makarantu A Jihar Kano Tayi

IMG 153335 03925 1756910028093

Daga Dr. Musa Tanko Haruna (Musa Mazankwarai)

Hakika nayi farin cikin ganin labarin umarnin da Mai girma Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bayar na rufe wasu makarantu guda takwas (8) da kuma gurfanar dasu gaban kuliya bisa tuhumar karya dokoki da ka’idojin gudanarwa. Wadannan kaidojin da aka rufe makarantun sabo dasu sun hada da karin kudin makaranta da rashin yin takardun izinin gudanarwa, rashin tsaro, rashin isassun tsarin gine-gine da sauransu. Makarantun da abin ya shafa sun hada da;

1. Prime College dake Alu Avenue
2. Darul Ulum dake Hotoro kan titin Ahmed Musa
3. Gwani Dan Zarga College dake Kofar Waika
4. Awwal Academy dake Rimi a Sumaila
5. Dano  Memorial College dake Sumaila
6. As-Saif college
7. Nurul Islam School
8. Unity Academy dake Wudil

Hakika wannan wani mataki ne daya dace ace duk wanda ke gudanar da harkar ilimi musamman makarantu masu zaman kansu suna biyayya ga ka’idojin da gwamnati ta gindaya.

Sai dai a daya bangaren, iyaye sun jima suna koke-koke dangane da wani salon yaudara da neman tursasa musu ta ko wane hali inda a yanzu an mayar da rubutu a cikin ‘TEXT’ books a maimakon littafin rubutu. Wannan wani tsarine da aka tsara littattafan da a ka’ida suna dauke da karatu da aikace-aikace (exercises) wanda ake bayar da umarni sannan idan akwai bukata sai a bawa dalibi aiki kona aji (class exercise) kona gida (homework) amma a shekarun baya kafin mayar da harkar ilimi ta zamo  jari hujja,  a cikin littafi (exercise books) ake rubutawa, amma saboda wasu dalilai wanda basa rasa nasaba da hadin baki tsakanin masu makarantu da masu buga litattafan, sai a tursasa aikin a cikin litattafan ta inda indai kana so yaronka ya koya dole sai ka siya, sannan  idan yaro yayi amfani dashi kuma malamai sukai rubutu da Jan biro hakan na hana yan uwan yaron suyi amfani dashi nan gaba.

Abinda zai baka mamaki a mafi yawancin lokuta, akan sami mutum daya yana da yara uku ko hudu a makaranta daya amma duk shekara sai ya siyi sabbin litattafai koda kuwa bai dace ba.

Sanin kowa ne cewa ada sai ka sami littafi kwaya daya amma kusan yara sama da 4 duk sunyi amfani dashi a gida ta yadda yaro yana gama aji za’a karbe litattafan a ajiyewa kannensa masu zuwa ajin dashi ya bari.

Amma idan ance duk aji sai an siya, hakan yasa iyaye basu da zabi dole su rinka siya duk shekara da makudan kudaden da dole sai an nemo su ko a ina suke. Shin me zai hana a koma yadda akeyi da?

Duba da irin wadannan koke-koke da wasu al’umma su kai a wasu sassa na Kasar nan.  An sami dacewar wasu Gwamnatocin Jihohi a Najeriya sun haramta rubutu cikin TEXT books ta yadda yara zasu rinka mora daga litattafan yan uwansu da suka wuce ajin da suke. Jihohin da suka hana wannan tsarin sun hada da

1. Jihar Banuwai wadda (itace ta farko)
2. Jihar Anambara ( da kashedin hana rubutu don na baya su mora
3. Jihar Edo ( Da kashedin za’a iya amfani dasu har tsawon shekaru hudu)
4. Jihar Imo (itama ta kayyade kamar yadda Edo tayi)
5. Jihar Ondo (Itama ta haramta sake siyan litattafai matsawar suna iya moruwa).

Ko shakka babu wadannan Jihohi sun yi abin a yaba musu kamar muma yadda muke da yakinin Insha Allah Mai Girman Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf zai saurari wannan koke-koken kamar yadda yake saurara kuma ya aiwatar.

Dan Allah Mai Girma Gwamna a kalli wannan batu daya dade yana yiwa iyaye kaikayi. Babu laifi, kuma abin alfaharine a garemu idan akace Jiharmu abar alfaharinmu Kano itace ta shida a jerin jihojin da suka dauki wannan mataki na soke rubutu cikin TEXT books.

Allah ya bada ikon aiwatarwa

Dr. Musa Tanko Haruna (Musa Mazankwarai)
Sashin Nazarin Kasa
Jami’ar Bayero, Kano

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *