Yanzu Yanzu: Gwamnan Kano Ya Shiga Ganawa da Shugaba Tinubu a Villa

IMG 170825 19126 1768838912804

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya shiga ganawar sirri da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, a fadar shugaban ƙasa da ke Aso Rock Villa, Abuja, a ranar Litinin, a daidai lokacin da ake ci gaba da jita-jitar shirin gwamnan na sauya sheƙa daga jam’iyyarsa ta NNPP zuwa jam’iyya mai mulki ta APC.

Ganawar ta gudana ne a ofishin shugaban ƙasa, inda Gwamna Abba Yusuf ya isa fadar da misalin ƙarfe 4:10 na yamma, sanye da farar babban riga (Agbada) tare da hular ja, abin da ya ja hankalin masu bibiyar al’amuran siyasa.

Tun makonnin baya, ana ta rade-radin cewa gwamnan Kano na dab da sauya sheƙa zuwa APC, lamarin da ya haifar da cece-kuce da rabuwar kai a tsakanin magoya bayansa, musamman dangane da alakarsa da jagoran siyasar NNPP kuma uban gidansa na siyasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Rahotanni sun nuna cewa tattaunawar sauya sheƙar ta ci karo da tangarda, sakamakon rashin jituwa kan batun tabbatar wa Gwamna Abba Yusuf tikitin takarar gwamna kai tsaye a zaɓen 2027, wanda ake cewa ya zama babban sharaɗi a cikin tattaunawar.

Masu sharhi na siyasa na ganin cewa wannan ganawa da Shugaba Tinubu ba ta rasa nasaba da shirin sauya sheƙar, duk da cewa babu wata sanarwa a hukumance daga bangarorin biyu har zuwa lokacin kammala wannan rahoto.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *