Za a Bude Wani Sabon Gidan Abinci, Kuma Zasu Raba Abinci Kyauta Ranar Laraba A Kano.

Alfijr

Alfijr ta rawaito za a bude wani sabon gidan abinci mai suna Dama Kitchen & Catering Services a Birnin Kano unguwar zoo Road.

Za a bude wannan gagarumin gidan abincin ne a ranar Laraba 11 ga watan Mayu 2022.

A zantawar Alfijr da shugabar gidan gidan abincin Haj Fatima Auny Dama, tace ranar Laraba rana ce da zasu dafa abincin su rabawa duk customer din da ya zo kyauta, don a tabbatar da ingancin abincin da dadinsa.

Auny Dama ta kara da cewar gidan abincin ya ƙunshi nau ikan kayan kwalam da makulashe daban daban cikin farashi mai sauki kuma.

Alfijr

Zaku iya samu wannan gidan abinci akan titin gidan zoo daura da Murtala suya, muna maraba da ku

Za a fara raba wannan abincin da karfe 4 na yamma bayan Sallar la asar idan Allah ya kaimu

Slide Up
x