Sanata Natasha ta bayyana ƙarin wasu tuhume, tuhumen da take yiwa shugaban majalisa Akpabio, a wata tattaunawa da tayi a gidan talabijin na ARISE
Natasha tace ta samu kiran waya da misalin karfe 12:14, daga sanata Bamidele, ya fara yi mata magana cikin girmamata da ƙasa da murya kuma ta yadda tabbas yana cikin firgici.
Yace mata, in kika matsa sai shugaban majalisa ya sauka daga kan matsayinsa ashirye yake yayi hakan, sunyi wannan wayar na tsawon mintuna biyu ne kacal kafin nan wani kiran ya ƙara shigowa da misalin karfe 12:26. Tana dubawa sai taga Akpabio ne da kansa ya kirata.
Tana ɗagawa yace, Sarauniyar majalisa da kanta, yayi mata bayani game da irin ƙalubalen da yake fuskanta a halin yanzu, yace mata yanzu haka matarsa kusan kwana biyu kenan ko bacci ba tayi saboda zagi da cin mutuncin da danginta suke mata duk a dalilin ki.
Sai tace, a a badai a dalilina ba sai dai a dalilinka, nifa Ban tilastaka kayimin wannan bayanin ba.
Yanzu dai Natasha tayi masa barazanar baiwa jami’ai damar fito mata da duk maganganun da su kayi da Akpabio domin ta watsawa duniya a cewar ta.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ