Ƙilu Ta Ja Bau! An Tumbuke Wani Alkali Bisa Ɗanyen Kai Daya Tafka

Alfijr ta rawaito wani babbar kotun jihar Kebbi ta kafa kwamiti da zai binciki zarge zargen da ake yi wa wasu alkalan kotunan biyu.

Alfijr Labarai

Ana zargin ɗaya daga cikinsu, Mustapha Umar Maccido da guduwa da ga bakin aiki yayin da wani Umar Salihu Kokami kuma, aka ce ya mari wani lauya da wasu mutane biyu.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban magatakarda na babbar kotun jihar Kebbi, Hussaini Abdullahi Zuru ya fitar a Birnin Kebbi a ranar Juma’a da ta gabata.

Ya ce tuni an dakatar da Umar Maccido, wanda ya daina zuwa aiki tun bayan da ya dauki hutun mako biyu, inda a ke zargin gano shi ya na yin alkalanci na zaman kansa na sirri a wani waje, duk da cewa shi babban alkali ne.

Zuru ya ƙara da cewa shi kuma Kokami, na Kotun Majistare ta III, Birnin Kebbi an dawo da shi zuwa shelkwata saboda karya ka’idar aiki

Alfijr Labarai

“An yi zargin cewa babban Alkalin Kotun Majistare Mustapha Umar Maccido ya gudu daga mukaminsa na Kotun Majistare, Kalgo, tun watan Satumban 2022, bayan karewar hutun sa na makonni biyu.

“An zarge shi da yin aiki na sirri a wasu gurare duk da cewa shi babban Alkali ne.

“Saboda haka, an dakatar da shi har sai an kammala rahoton kwamitin gudanarwa da aka kafa don bincikar lamarin,” in ji sanarwar.

Abdullahi Zuru ya kara da cewa, an dawo da Salihu Kokani na Kotun Majistare ta III, Birnin Kebbi zuwa hedikwatar saboda rashin da’a a aiki.

Ya ce: “Akwai zargin da babban Lauya kuma babban sakatare na ma’aikatar shari’a ya yi masa na rashin da’a, cewa a ranar 12 ga watan Satumba, ya mari wani Lauyan jihar, Abdullahi Bawa Dan Bauchi da wasu mutane biyu.

Alfijr Labarai

Wannan matakin ya faru ne a harabar babbar kotun majistare ta daya, a Birnin Kebbi, wadda aka ba shi alhakin karbar shari’ar wasu ma’aikatan ma’aikatar ilimi mai zurfi.

Don haka, ofishin babban magatakardar na bayar da umurnin a sake kiransa zuwa hedkwatar, har sai an kammala rahoton kwamitin gudanarwa da aka kafa domin binciken lamarin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *