Ƙarfin Hali: An kama wasu matasa biyu bisa yunƙurin mika tabar wiwi ga daurarru a kotun Kano

FB IMG 1767798916111

Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta ƙasa , reshen jihar Kano, ta kama wasu matasa biyu bisa zargin yunƙurin shigar da ƙwayoyi  ga fursunoni a harabar kotun Nomansland da ke Kano.

An bayyana sunayen waɗanda ake zargin da Usman Khalid mai shekaru 25 da Bello Musa Ahmed mai shekaru 24, dukkaninsu mazauna unguwar Tsamiya (Breget) a Jihar Kano.

Jami’an hukumar da ke aiki a Cibiyar tsare fursunoni ta Goron Dutse, ne suka kama su yayin da suke ƙoƙarin jefa ganyen wiwi (da wasu ƙwayoyi  ga fursunoni a harabar kotun.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Musbahu Lawan Kofar Nasarawa ya fitar, hukumar ta gargaɗi al’umma da su guji cudanya da fursunoni, musamman a lokacin kai su kotu ko dawo da su daga kotu, tana mai cewa hakan babban barazana ne ga tsaro kuma doka ta tanadi hukunci a kai.

Kwanturola na hukumar kula da gidajen gyaran hali ta ƙasa a jihar Kano, Ado Inuwa, ya bayar da umarnin a mika waɗanda ake zargi tare da ƙwayoyin da aka kama ga hukumar yaki da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) domin gudanar da bincike da gurfanar da su a gaban shari’a.

Hukumar ta jaddada aniyarta ta tabbatar da tsaro da kuma aiwatar da manufar ƙin amincewa da duk wani abu da ya shafi ƙwayoyi  a cibiyoyin tsare fursunoni da harabar kotuna a faɗin Jihar Kano. Haka kuma, ta bukaci jama’a da su bai wa hukumomin tsaro haɗin kai domin tabbatar da zaman lafiya da doka a jihar.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *