Ƙasar Faransa ta tattauna da jami’ai a Nijar kan kwashe sojojin ta

sojojin Faransa suna tattaunawa da sojojin Nijar kan ficewar “wani bangare” na sojojin daga kasar bayan juyin mulki.

Alfijir Labarai ta rawaito Faransa ta fara magana da wasu jami’an sojojin Nijar kan janye wasu dakarunta daga Nijar bayan juyin mulkin watan Yuli, kamar yadda jaridar Le Monde ta ruwaito.

Ba a yi tattaunawar da jagororin juyin mulkin ba, amma an yi da wasu sojoji da ke aiki da Faransa tsawon lokaci, kamar yadda jaridar ta ce a ranar Talata.

Wata majiya a ma’aikatar tsaro ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa sojojin Faransa suna tattaunawa da sojojin Nijar kan ficewar “wani bangare” na sojojin daga kasar bayan juyin mulki.

“An fara tattaunawa kan yadda za a fitar da wani bangare na sojojin daga kasar,” kamar yadda majiyar wanda ba ta so a bayyana sunanta ta bayyana.

Sai dai majiyar ba ta yi karin bayani ba. Tun da farko, wata majiya a kusa da Ministan Tsaro Sebastien Lecornu ta shaida wa AFP cewa ana kan tattaunawa “wadda za ta taimaka wajen fitar da sojojin Nijar” a Nijar.

Majiyar ta ce “an fitar da sojojin Faransa daga kasar tun bayan dakatar da aikin hadin gwiwa kan yaki da ta’addanci” biyo bayan juyin mulkin.

Akwai jita-jita da ke cewa zai zama dole ga Faransa ta fice gaba daya daga Nijar bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yuli, wanda ya hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum wanda babban abokin huldar Faransa ne.

Biyo bayan juyin mulkin, Faransa wacce ita ce ta yi wa Nijar mulkin mallaka, ta ce za ta kawo karshen aikin hadin gwiwar soji da kasar da kuma dakatar da duk wani taimako da take bai wa kasar.

Sai dai Faransa ta yi watsi da kiraye-kirayen jagororin juyin mulkin na kwashe dakaru 1,500 wadanda suke Nijar a halin yanzu, ta ce har yanzu zababben Shugaba Bazoum ta sani, wanda aka yi wa daurin talala, a matsayin halartaccen zaben shugaban kasar.

Ma’aikatar tsaron Faransa ba ta amsa sakon da aka tura mata ba.

Yaki da masu tayar da kayar baya
Firai Ministan Nijar wanda sojoji suka nada Ali Mahaman Lamine Zeine ya ce a ranar Litinin an fara “tuntuba cikin hanzari” don barin dakarun Faransa daga Nijar.

Haka zalika Zeine ya ce muna fatan “ci gaba da hulda idan zai yiwu da kasar da muke da abubuwa iri daya.” Kamar yadda Le Monde ta bayyana cewa za a mayar da dakarun Faransa da ke Nijar wani wuri a yankin, a kasar Chadi mai makwabtaka, yayin da za a mayar da wasu kasar Faransa.

Dubban masu zanga-zanga sun taru a gaban sansanin sojojjn Faransa a babban birnin Nijar, Yammai a ranar Asabar da ta wuce, inda suke kiraye-kirayen sojojin su fice daga kasar.

Ficewar sojojin daga Nijar cikas ne ga ikon da Faransa take da shi a yankin, bayan ficewarsu daga Mali, inda sojojin hayan Rasha suka maye gurbinsu.

Nijar tana aikin hadin gwiwar tsaro da Faransa da Amurka, wadda take amfani da sansaninta wajen yaki da masu tayar da kayar baya a yankin Yammacin Afirka da Sahel.

Dakarun Faransan suna da sansani ne a kusa da birnin Yammai, inda a ‘yan kwanakin nan ya zama wurin da dubban mutane suke zanga-zangar neman su fice daga kasar.

TRT World

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@musa_bestseller

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *