Daga A’isha Salisu Ishaq
Saudiyya ta bai wa gwamnatin Najeriya kyautar tan 100 na dabino a matsayin tallafin da ta saba bayarwa duk shekara.
Wata sanarwa da ofishin jakadancin ƙasar a Najeriya ya fitar ranar Litinin ta ce tallafin kyauta ce daga Sarki Salman na Saudiyya.
Sanarwar ta ƙara da cewa jakadan Saudiyya a Najeriya, Faisal Al-Ghamdi, shi ne ya jagoranci miƙa kyautar, wadda aka bayar ta hannun ƙungiyar King Salman Humanitarian Aid and Relief Centre (KSrelief) domin taimaka wa talakawa.
“Jakada Al-Ghamdi ya yi bayanin cewa a wannan shekarar an ba wa Abuja tan 50, Kano ma tan 50,” in ji sanarwar.
BBC
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ