Alfijr ta rawaito wasu ƴan bindiga da ake kyautata zaton sun sace daliban jami’ar Nsukka (UNN) da dama da ke komawa makarantar bayan yajin aikin watanni takwas da kungiyar malaman jami’o’i ta yi.
Alfijr Labarai
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 4 na yammacin ranar Lahadi, 23 ga watan Oktoba, 2022, a kan titin Nsukka-Opi, Ekwegbe, al’ummar karamar hukumar Igbo-Etiti a jihar Enugu, a kudu maso gabashin Najeriya.
An tattaro cewa ‘yan bindigar sun yi garkuwa da matafiya a kan hanyar tun da yammacin ranar Asabar.
Rahoton yace, an kuma ce an ci gaba da kai hare-hare a kan hanyar a ranar Talata, 25 ga Oktoba, 2022.
Wasu masu sa’a da suka yi nasarar tserewa, sun ce masu garkuwa da mutanen sun far wa motocin bas na kasuwanci akalla guda shida, tare da yi musu harsasai tare da karkatar da mutanen zuwa cikin dazuzzuka.
Alfijr Labarai
An tattaro cewa tuni masu garkuwan suka fara tuntubar iyalan wadanda abin ya shafa, suna neman a biya su Naira miliyan 30.
Wata majiya ta bayyana cewa wata mata daga Aku da ke karamar hukumar Igbo-Etiti a jihar Enugu da dansa na cikin wadanda lamarin ya rutsa da su, inda ta kara da cewa yayin da aka sako dan, matar tana hannun riga.
Hakazalika ya ce wani likitan da ya samu ‘yanci ya biya kudin fansa da ba a bayyana ba domin a ‘yanta shi.
Ya kuma bayyana mamakinsa yadda irin wannan aika-aikar za ta iya faruwa a kan titin da shingayen tsaro kusan shida tsakanin Nike da Opi Junction a karamar hukumar Nsukka ta jihar Enugu. Rundunar ‘yan sanda a jihar Enugu ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce sun baza jami’an tsaro da na sirri a yankin domin tabbatar da isasshen tsaro a hanyar da kuma ceto wadanda aka sace.
Alfijr Labarai
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Daniel Ndukwe, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Laraba, 26 ga watan Oktoba, 2022, ya ce har yanzu ba a tantance adadin wadanda aka sace ba.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ahmed Ammani, ya bayar da umarnin tura jami’an ne biyo bayan samun bayanan da suka yi game da garkuwar, Mista Ndukwe ya ce.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
iR News