Ƴan Sanda Sun Kama Tsohon Jami’in Tsaro Kan Zargin Barazanar Kisa Ga Yakubu Dogara

Alfijr ta rawaito kwamishinan ƴan sanda na jihar Bauchi, Umar Sanda ya ce rundunar ta kama tsohon mai kula da makamai, sakamakon faɗaɗa bincike kan ikirarin da tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya yi na barazana ga rayuwarsa.

Alfijr Labarai

Sanda ya shaida wa manema labarai a jiya Lahadi a Bauchi cewa an kama tsohon jami’in tsaron ne bisa zargin ɓatan bindigogi daga rumbun ajiyar makamai na rundunar.

Sanda ya ce ya bayar da umarnin a binciki ma’ajiyar makamai ta rundunar, ya ƙara da cewa baya ga bindigu biyu da aka kama, ba a ga ƙwaya ɗaya ba.

“Mun faɗaɗa bincikenmu,” in ji shi, ya kara da cewa jami’in kula da kayan yaki da aka kama ya bar aikin shekaru biyu da suka gabata.

Alfijr Labarai

Dogara dai ya kai kara zuwa ga Sufeto-Janar na ƴan sandan kasar, inda ya zargi ƴan sanda biyu da wani farar hula ɗaya da suka hada baki domin su ɓatar da shi.

“Har yanzu ba mu tabbatar da ikirarin ba saboda daga bakin mutum daya ya fito, amma mun tsananta bincike,” in ji kwamishinan ƴan sandan.

Sanda ya ƙara da cewa “Za mu shaida wa duniya sakamakon binciken da zarar mun gama da shi, babu wani abu da za mu boye.”

Daily Nigerian

Slide Up
x