Gwamna  Ganduje Ya Jajantawa Iyalan Fitaccen Dan kasuwa Alh Uba Leader

Alfijr ta rawaito Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya jajantawa iyalansa bisa rasuwar fitaccen dan kasuwa kuma hamshakin attajiri Alh. Uba.

Alfijr Labarai

Gwamnan a sakon da mataimakinsa kuma dan takarar gwamna Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya mika a madadinsa wanda ya jagoranci tawagar gwamnatin jihar wajen jana’izar marigayin ya bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ba ga jihar Kano kadai ba har ma da kasa baki daya.

Gwamna Ganduje wanda ya kuma jajantawa ’yan kasuwar game da rasuwar mai taimakon ya ce Alh.Uba Leader yana cikin ’yan kasuwar da suka bayar da gudunmawa wajen ci gaban tattalin arziki da mayar da Kano cibiyar jijiyar kasuwanci a Arewacin Najeriya.

Ya yi rayuwa ta hidimar rashin son kai yana ba da gudummawa ga bil’adama ta hanyar ayyukan jin kai na samar da ayyukan yi ga marasa galihu.

Alfijr Labarai

Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya gafarta masa ayyukansa, ya ba shi Jannatul Firdaus, ya kuma baiwa iyalansa hakurin jure rashin da ba za a iya kwatantawa ba.

Tawagar gwamnatin jihar ta hada da matakin dan takarar gwamna na jam’iyyar APC Alh.Murtala Sule Garo da kwamishinoni da sauran manyan jami’an gwamnati.

Kamar yadda Hassan Musa Fagge Babban Sakataren Yada Labarai na Mataimakin Gwamnan Kano Ya fitar

Slide Up
x