Alfijr ta rawaito Rundunar ‘yan sandan jihar ta bayyana cewa tana neman dan takarar gwamna ‘yan kwanaki kafin zabe.

Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressive Grand Alliance (APGA) a jihar Ebonyi, Ifeanyi Odoh, ya shiga hannun rundunar ‘yan sandan jihar bisa zargin kashe wani sarki, Igbokwe Ewa.
An bayyana Odoh da sauran su ne, bayan da jam’iyyar APC mai mulki ta zarge su da daukar nauyin kashe sarkin.
Har sai da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka harbe shi a makon da ya gabata a ranar Litinin.

Sarkin ya kasance basaraken al’ummar Umu-Ezekoha da ke karamar hukumar Ezza ta Arewa a jihar.
Sai dai Odoh ya musanta zargin da kakkausar murya, inda ya bayyana cewa sarkin wanda ya fito daga karamar hukuma daya tare da shi tamkar uba ne a gare shi.
Sai dai rundunar ‘yan sandan jihar ta bayyana cewa tana neman sa tare da wasu mutane tara, dangane da kisan da aka yi wa sarkin.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Onome Onovwakpoyeya, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau.

Ya ce: “Rundunar ‘yan sandan jihar Ebonyi ta bayyana wadanda ake nema ruwa a jallo a kan kisan da aka yi wa mai martaba Eze Christopher Igboke Ewa na yankin Umu-Ezekoha a Ezza ta Arewa.”
Ya lissafa wasu a cikin wadanda ake nema sun hada da: Samuel Onyekachi Aligwe, Peter Orogwu (wanda aka fi sani da yaro daya), Chukwudi Aliewa (aka Ezza) da Chika Ezealigbo, Sauran su ne : Nnaemeka Egede (aka Champaign), Nnabuike Okohu, Ogobuchi Agbom (aka Okiri). ,
Nonso Obasi, Ikechukwu Nwoba (aka Solid).
The Nation ta bayyana cewa a karshen shekarar da ta gabata ne aka kai wa Odoh da ayarin sa hari a karamar hukumar Izzi.
Ko da yake ba a samu asarar rai ba a wannan harin, daya daga cikin motocin da ke cikin ayarin nasa ya lalace sakamakon harbin bindiga da maharan suka yi.

Odoh ya sake fuskantar wani mummunan hari a karamar hukumar Ishielu, in da dan sanda da direbansa suka mutu.
Hakazalika wasu ‘yan bindiga sun kai hari gidan dan takarar majalisar wakilai na jam’iyyar PDP a mazabar Izzi/Abakaliki, Barnabas Ofoke.
An lalata motoci da wasu kayayyaki masu daraja a harabar da aka yi amfani da su wajen yakin neman zaben dan takarar gwamna na jam’iyyar, Ifeanyi Odii.
An kuma kashe wani mai goyon bayan jam’iyyar APC a watan da ya gabata a karamar hukumar Íshielu yayin da wasu ‘yan bindiga suka bude wuta a wani filin yakin neman zabe a yankin.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, Odoh bai samu damar jin ta bakinsa ba, kamar yadda mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Charles Otu shi ma ya kasa amsa kiran da aka yi masa a lambobin wayarsa a lokacin da aka gabatar da rahoton.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai