Daf Nake Da Warware Rikicin Dake Faruwa A Kano! Inji Mai Mala Buni

Alfijir

Alfijir

kwamitin tsare-tsare na rikon kwarya da Buni ke jagoranta ya tsunduma cikin kokarin kawo karshen rikicin da ke faruwa a jam iyyar APC ta Kano.

jaridar PUNCH ta ruwaito cewa wasu masu ruwa da tsaki na jam’iyyar karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau sun yi kaca-kaca da wani bangaren masu biyayya ga gwamna mai ci Abdullahi Ganduje.

A cewarsa, masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar Kano a yau sun gana a dakin taro na gwamnan Yobe dake Abuja domin ci gaba da sasanta al’amura daban-daban a jihar.

Taron ya kasance karkashin jagorancin shugaban kwamitin riko da gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni.

Sanata Ibrahim Shekarau, Barau Jibrin, Kabiru Gaya, shugaban masu rinjaye, majalisar wakilai, Hon. Alhassan Ado Doguwa da wasu wakilan gwamnatin jihar ne suka halarci taron.

Mahalarta taron sun nuna gamsuwa da tsarin kuma sun kasance da fatan cewa za a warware duk bambance-bambancen.”

Slide Up
x