Gwamnatin Tarayya ta Amince Da Dawowar Aikin Jirgin Emirates Zuwa Najeriya.

Alfijir

Alfijir

Alfijir ta rawaito, gwamnatin Najeriya ta amince da jirgin sama na Emirates da ke Dubai su koma jigila a kasar kowane lokaci daga yanzu, shi kuma kamfanin jirgin Air Peace da ke Najeriyar shi ma ya ce zai koma safara zuwa Dubai, daga ranar1 ga watan Maris na 2022.

Trust Tv ta ce, hukumar kula da sufurin jirgin sama ta Najeriya (NCAA) mai dauke da sa hannun shugabanta, Captain Musa Nuhu ta rubuta wa shugaban hukumar sufurin jirgin sama ta kasar Dubai, Saif Mohammed Al Suwaid.

Alfijir

Wasikar da hukumar ta aike ta ce, bayan nazarin da hukumomin da abin ya shafa suka a kan dokokin kariya na korona da hukumomin na Dubai suka gindaya, a yanzu Najeriya ta amince da cigaba da sufuri a kasar.

Idan za a iya tunawa wa’annan matakin ya biyo baya ne sakamakon bullar kwayar cutar korona nau’in Omicron a karshe-karshen shekarar da ta gabata, hukumomin Hadaddiyar Daular Larabawan sun takaita sufurin fasinjoji zuwa kasar daga Najeriya da wasu kasashen Afirka 11, dokar da ta dage ranar 29 ga watan Janairun shekaran nan.

Alfijir

Najeriya da Dubai sun sasanta sabanin da aka samu a tsakaninsu kan gwajin cutar korona da kuma daga bisani sabani kan yawan jiragen da za su rika sufuri a tsakanin kasashen biyu.

Jirgin na Dubai yana zuwa Najeriya sau 21 a mako, yayin da Air Peace na Najeriya ke zuwa can sau bakwai a sati.

Slide Up
x