Alfijr ta rawaito wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu ‘yan uwa biyu na gidan Dagacin kauyen Nasarawa da ke karamar hukumar Tsanyawa a jihar Kano.

Wadanda aka yi garkuwa da su sun hada da matarsa, Halima Kabiru mai shekaru 38 da Dahiru Kabiru mai shekaru 20.
CP Mamman Dauda, shine kwamishinan ‘yan sanda a jihar, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) garkuwa da mutanen.
“Bayan samun bayanin, nan da nan muka kafa tawagar ceto a sassan da ke makwabtaka da su.”
A yayin da muke magana da ku yanzu haka, tawagar tana aiki tukuru don ceto wadanda lamarin ya shafa ba tare da sun ji rauni ba,” inji shi.
Ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, amma ya nuna kwarin gwiwar cewa za a kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su, tare da kama wadanda suka yi garkuwa da su din.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇