Gwamnan Kano Ya Tabbatarwa Da Farfesa Adamu Gwarzo Haɗin Guiwar Jihar Da Jami oinsu

Alfijir Labarai ta rawaito Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ce jihar za ta hada gwiwa da manyan jami’o’i masu zaman kansu a ciki da wajen kasar nan domin ci gaban jama’a.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ranar Litinin a gidan gwamnatin Kano a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban kungiyar jami’o’in Afirka masu zaman kansu Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo.

Abba Kabir Yusuf ya bayyana Farfesa Gwarzo a matsayin hamshakin dan kasuwa a fannin ilimi wanda kuma ke kokarin inganta makarantun gaba da sakandare duk da karancin jarin da yake samu.

Ya kuma yaba da kokarin Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo a kokarinsa na samar da ilimin jami’a mai zaman kansa a farashi mai rahusa.

Tun da farko, Farfesa Gwarzo ya ce ya ziyarci gwamnan da mataimakinsa ne domin gabatar da takardar shaidar wasu jami’o’i masu zaman kansu guda biyu da ya samu (Franco-British International University, Kaduna da Canadian University of Nigeria, Abuja).

Wannan ya sa ya zama babban mai jami’a mai zaman kansa a Afirka wanda ke gudanar da jami’o’i hudu a Kano, Maradi, Kaduna da Abuja.

Edu-preneur ya kuma yi alkawarin tallafa wa jami’o’in jihohin biyu don inganta koyo, halayya da bincike cikin yanayi mai kyau.

Kamar yadda Sanusi Bature Dawakin Tofa Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar Kano ya wallafa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *