Bayan garkuwa da mutum 11 a Dutse-Alhaji, ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu mutum 23, a Bwari yan bindiga sun yi garkuwa da Kwamishinan Inganta Rayuwar Matasa na Jihar Anambra, Patrick Agha Mba, sun kuma yi awon-gaba har da matar sa, bayan sun bindige ɗaya daga cikin hadiman sa, a ranar Juma’a.
Alfijir labarai ta ruwaito an bayanan sunan hadimin wanda aka bindige da Ernest Offiah, wanda lauya ne.
Bayanai sun tabbatar da maharan sun tare hanyar ne inda suka yi awon-gaba da kwamishinan da matar sa, lokacin da suke kan hanyar zuwa halartar bikin aure a Abuja, auren Adaora, ‘yar Gwamna Charles Soludo na Jihar Anambra.
An dai yi bikin a makon da ya gabata a Isuofia, cikin Ƙaramar Hukumar Aguata, a Jihar Anambra.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj