Daga Aminu Bala Madobi
Tun bayan fitar hoton gwamnan jihar Kogi, Usman Ododo na APC, ya haifar da doguwar muhawara akar sada zumunta bayan da ya halarci taron liyafar cin abincin dare da gwamnonin jam’iyyar PDP suka gudanar a jihar Taraba.
Alfijir Labarai ta rawaito Ododo da aka gani a wani hoton da Ahmadu Fintiri, gwamnan Adamawa ya saka a ranar Asabar, yana sanye da irin wadannan riguna da takwarorinsa na abincin dare na Gala da ke nuna dimbin al’adun Taraba,” in ji Fintiri a cikin sakon.
Gangamin taron da gwamnonin PDP suka gudanar ya kasance rana ce da kotun koli ta tabbatar da nasarar Ododo, dan jam’iyyar APC) a matsayin zababben gwamnan Kogi.
Kotun kolin ta yi watsi da daukaka karar Murtala Ajaka, dan takarar gwamna na jam’iyyar SDP a jihar, wanda ya kalubalanci nasarar Ododo.
Duk da cewa Ododo ya halarci bikin auren diyar gwamnan Taraba, kasancewar sa a cikin gwamnonin PDP ya haifar da zazzafan martani ta yanar gizo.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj