Jam’iyyar PDP Ta Tabbatar Da Dakatar Da Sanata Umaru Tsauri Daga Jam’iyyar daga Mazabar Tsauri A

Sanata Tsauri

Shugaban jam’iyyar PDP Dan Jume Abdussalam kumare ya samu Takardar dakatarwar gada Chairman Na Mazabar Tsauri A Dandume tare Da Sanya Hannun Shugabanin Jam’iyyar PDP na mazabar Tsauri dake Karamar Hukumar Kurfi,  Dan Jume Abubakar ne ya tabbatarwa wakilin Alfijir Labarai hakan.

Alfijir Labarai ta rawaiti shugaban jam’iyyar PDP ya kuma tabbatar da cewar bayan dogon zama da shugaban da sauran Exco suka yi akan lamarin, a karshe dai sun yi wannan hukuncin dakatarwar ne domin wasu dabiu, da  rikici tare da rashin zaman lafiya da yake haifarwa a wannan jam’iyyar, ko ya nutsu ya gyara halinsa.

Shima shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Katsina Hon. Nura Amadi Kurfi ya tabbatar da wannan hukuncin Kamar Yanda ya samu daga mazabar Tsauri, ya kuma kara da cewar, mun kama shima da yiwa jam’iyyar zagon kasa a zaben gwamna Da Sauransu inda yayi anti party Da fatanci ga Shugabanci Jam’iyyar PDP Na Kasa tare Da fatanci ga mutane masu mutunci na son shigowa jam’iyyar amma saboda shi abin ya gagara.

Hakazalika shugabannin sun ce wannan hukuncin da fatan zai zama izna ga sauran yan jam’iyyar PDP masu hali irin nasa da su zauna lafiya su kuma cigaba da kawowa jam’iyyar dauki wajen maganin mulkin yan kama karya a Jihar.

Cikakken Bayani
👇👇👇👇

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *