Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da sunayen waɗanda aka zaɓa domin zama a kwamitin farko na hukumar cigaban Yankin Arewa Maso Yamma (NWDC) ga majalisar dattijai domin tantancewa.
Alfijir labarai ta rawaito wannan na biyo bayan sanya hannu kan ƙudirin dokar kafa NWDC da shugaban ya yi a ranar 24 ga Yuli, 2024, a matsayin muhimmin mataki wajen kafuwar hukumar.
Sunayen waɗanda aka naɗa sun haɗa da:
Shugaba: Ambasada Haruna Ginsau (Jigawa)
MD/CEO: Farfesa Abdullahi Shehu Ma’aji (Kano)
Mambobi:
Dr. Yahaya Umar Namahe (Sokoto)
Hon. Aminu Suleiman (Kebbi)
San. Tijani Yahaya Kaura (Zamfara)
Hon. Abdulkadir S. Usman (Kaduna)
Hon. Engr. Muhammad Ali Wudil (Kano)
Shamsu Sule (Katsina)
Nasidi Ali (Jigawa)
Hukumar za ta mayar da hankali wajen samar da cigaban tattalin arziki, bunƙasa rayuwa da cigaban zamantakewa a yankin Arewa Maso Yamma.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj