Manhajar TikTok ta goge bidiyo miliyan 2.1 a ƙasar Najeriya

Tiktok

Shafin TikTok ya ce ya goge bidiyoyi sama da miliyan 2.1 a Najeriya a cikin wata shida na farkon 2024 saboda saɓa ƙa’idojinsu.

Alfijir labarai ta rawaito kamar yadda rahoton tabbatar da bin dokokin amfani kafar da aka kamfanin ya fitar a ranar Talata ya nuna, kamfanin ya ce ya ɗauki matakin ne a cikin ƙoƙarin da yake yi na tabbatar da samar da daidaito da kuma tsabtace kafar.

“Bincike ya nuna cewa kashi 99.1 na bidiyoyin nan an cire su ne tun kafin a kawo ƙarar su, sannan kashi 90.7 an cire su ne a cikin awa 24. Waɗannan alƙaluman suna tabbatar da ƙoƙarin kamfanin TikTok na hana yaɗa abubuwa marasa kyau, domin tabbatar da samar da kafa mai kyau ga ma’abota kafar a Najeriya,” kamar yadda rahoton ya nuna.

Sai dai waɗannan bidiyoyin da aka goge ba su ma kai kashi ɗaya cikin ɗari ba na bidiyoyin da ƴan Najeriya suka ɗora a zamanin watannin da aka yi nazari domin wannan rahoton.

A duniya, TikTok ta ce ta cire sama da bidiyoyi miliyan 178 a watan Yunin 2024, inda ta ce bidiyoyi miliyan 144 daga ciki kwamfuta ce ta goge su.

BBC

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *