An Sami Ambaliyar Ruwa A Gonakin Shinkafa A Jihar Kwara

IMG 20250126 214155

Gwamnatin Jihar Kwara ta bayyana damuwarta kan ambaliyar rowa a gonakin shinkafa da dama a Shonga, da ke karamar hukumar Edu ta jihar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamna Rafiu Ajakaye ya fitar,  ya ce  Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya  kafa kwamitin da zai binciki musabbabin ambaliyar.

A cewarsa ana sa ran kwamitin zai ziyarci yankunan da lamarin ya shafa domin gudanar da bincike.

Sanarwar ta ce kwamitin zai kai ziyarar jaje ga Sarkin Shonga Dr. Haliru Yahyah da wadanda abin ya shafa a cikin al’umma.

Mambobin kwamitin da mataimakiyar shugaban ma’aikatan jihar, Gimbiya Bukola Babalola za ta jagoranta, sun hada da kwamishinan ayyukan gona, Mrs Oloruntoyosi Thomas, da kwamishinan muhalli, Hajiya Nafisat Musa Buge; da mai ba da shawara na musamman kan ayyuka na musamman; da  tsaro ga Gwamna,  Alhaji Muhyideen Aliu, da sauransu.

RN

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *