Kwankwaso ya caccaki yan sanda kan yunkurin hana mauludin Tijjaniyya a Kano

Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya taya Darikar Tijjaniyya murnar kammala taron Mauludin Sheikh Ibrahim Inyass da aka gudanar a  filin wasa na Sani Abacha a jihar Kano, inda ya ce an gudanar da mauludin cikin nasara.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X , Kwankwaso ya mika sakon taya murna ga manyan shugabanni masu ruwa da tsaki, ciki har da Mai Martaba Khalifa Muhammad Sanusi II, Sarkin Kano, da Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano, kan shirya wannan babbar taro mai tarihi.

Sai dai, Kwankwaso ya nuna damuwarsa kan wani “gargadin kai harin ta’addanci” da rundunar ‘yansandan jihar Kano ta fitar a daren gabanin taron, inda ya soki wannan gargadi, yana mai cewa bai dace ba, kuma yana iya yin barazana ga nasarar taron tare da jefa tsoro a zukatan mazauna jihar da baki daga kasashen waje.

“Wannan hali na ‘yan sanda ba kawai ya jefa rayukan mutane a Kano cikin hadari ba, har ma ya bata sunan rundunar ‘yan sandan Najeriya a idon duniya, musamman ganin muhimmancin taron Mauludi a matakin kasa da kasa,” in ji shi.

Kwankwaso ya nuna cewa irin wadannan gargadin ƙarya na karya za su iya sanya mutane yin sakaci idan wata barazana ta gaskiya ta taso a nan gaba. Haka nan ya zargi ‘yan sanda da nuna bangaranci tare da alakanta ayyukansu da wani shirin gwamnatin tarayya na tsoma baki a harkokin jihar Kano

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *