Gwamnatin Jihar Kwara ta bayyana damuwarta kan ambaliyar rowa a gonakin shinkafa da dama a Shonga, da ke karamar hukumar Edu ta jihar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamna Rafiu Ajakaye ya fitar, ya ce Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya kafa kwamitin da zai binciki musabbabin ambaliyar.
A cewarsa ana sa ran kwamitin zai ziyarci yankunan da lamarin ya shafa domin gudanar da bincike.
Sanarwar ta ce kwamitin zai kai ziyarar jaje ga Sarkin Shonga Dr. Haliru Yahyah da wadanda abin ya shafa a cikin al’umma.
Mambobin kwamitin da mataimakiyar shugaban ma’aikatan jihar, Gimbiya Bukola Babalola za ta jagoranta, sun hada da kwamishinan ayyukan gona, Mrs Oloruntoyosi Thomas, da kwamishinan muhalli, Hajiya Nafisat Musa Buge; da mai ba da shawara na musamman kan ayyuka na musamman; da tsaro ga Gwamna, Alhaji Muhyideen Aliu, da sauransu.
RN
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ