A Yau 4 Ga Watan Oct 2025 Gamayyar Kungiyoyin Jam’iyyar Apc Na Jihar Kano guda 12, kamar haka
1- Kano State Apc Integrity Group
2- Kano State Apc Amalgamation Forum
3- Apc Interlactual Forum
4- Ganduje Support Group
5- Apc Concern Forum
6- Apc Media Inlightment Forum
7- Abdullahi Abbas Political Vanguard
8- Tinubu/Shettma Political Movement
9- Kano State Apc Mager
10- Apc Kano Central Movement
11-Gawuna/Garo Political Aweirness
12- Apc Dan Sarki Organization
Mun shirya wannan ganawa da manema labarai bisa abubuwan da suke faruwa a jihar mu ta Kano mai albarka biyo bayan janyewar yan sanda daga bikin cikar najeriya shekaru 65 da samun yancin kai.
Sakamakon wanann janyewa ta yan sanda mai cike da alamun tambaya, mai girma gwamna ya nemi da a dauke shugaban yan sandan.
Saboda haka muna goyon bayan wannan kira na gwamna Abba Kabir, kuma muna barranta kan mu daga zanga-zangar nuna goyon baya ga kwamishinan yan sandan na jihar Kano [CP Bakori] wanda wasu kungiyoyin jam’iyyar APC suka yi bisa da’awar cewa al’ummar jihar Kano ne.
Wadanda suka yi wannan zanga-zangar Ta Nuna Goyon Baya Ga Kwamishinan yan sanda na jihar Kano [Cp Bakori] kungiyoyi ne na jam’iyyar APC da aka dauki nauyinsu, kamar yadda muma an neme mu da muyi hakan, amma mukaga rashin dacewar hakan, saboda a baya ma anyi amfani da irin wannan hanya wajen rura wutar rikicin masarauta.
Saboda Haka muna sanar da shugabancin jam’iyyar APC na jihar Kano dama dukkan yayan jam’iyyar da a daina siyasantar da har-kar tsaro da har-kar masarauta ta hanyar da sunan al’ummar jihar Kano !
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t