Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rantsar da sabbin kwamishinoni biyu da Babban Lauya na Jiha, wadanda za su kasance cikin Majalisar Zartarwa ta Jihar.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin-Tofa, ya fitar a ranar Juma’a a Kano.
Sabbin kwamishinonin da aka rantsar sun hada da Abdulkarim Maude, SAN, a matsayin Kwamishinan Shari’a kuma Babban Antoni Janar, da kuma Farfesa Aliyu Isah, a matsayin Kwamishinan Harkokin Kiwo.
Haka kuma, an rantsar da Salisu Tahir a matsayin Babban Lauya na Jiha (Solicitor-General) kuma babban Sakatare na Ma’aikatar Shari’a.
An gudanar da bikin rantsuwar ne a yayin bude taron Majalisar Zartarwa ta Jiha karo na 32, da aka gudanar a Fadar Gwamnati da ke Kwankwasiyya City.
Gwamna Yusuf ya umarci sabbin jami’an da su yi aiki da jajircewa, gaskiya da tawali’u, yana mai jaddada muhimmancin aiki tare domin cimma burin gwamnati.
Ya kuma sake tabbatar da kudirin gwamnatinsa na bai wa ci gaban ababen more rayuwa da ilimi da kiwon lafiya da tsaro da karfafa gwiwar jama’a da samar da ayyukan yi muhimmanci, tare da alkawarin ci gaba da aiki tukuru don inganta rayuwar al’umma.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t